Yanda zaka gano mai ma bincike a wayarka
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan App din clock, wannan Application din zai baka damar boye duk wani sirrinka na wayarka kamar su photos videos files da sauransu. Dan haka na tabbata da wannan Application din zai taimaka muku sosai.
Clock , Application ne wanda zai baka damarmaki da yawa. Na daya boye dukkanin sirrukanka, na biyu zai kama maka duk wanda yake yi maka bincike a wayarka. Na uku zai baka damar bude shi (Application) da password na bogi
Dan haka zai burge ku sosai
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.