Yanda zaka karawa wayarka Sauri da saurin Internet
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan App din killApp, wannan Application din zai baka damar karawa wayarka sauri, domin nasan mutane da yawa suna fama da wannan matsalar. Dan haka na tabbata da wannan Application din zai taimaka muku sosai.
KillApp, Application ne wanda zai baka Tsaida duk wasu Application da suke kamar maka da wayarka, domin akwai Application da suke amfani a background na waya kamar whatsApp, facebook, Instagram da sauransu.
Wannan Application din zai tsaida duk wani Abu da yake tsaida maka wayarka.
Dan haka zai burge ku sosai
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.
Comments
Post a Comment