Yanda zaka dau kowani bidiyo ko sauti a sirrance
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani.
Wannan wani Application ne?
Hakika wannan Application din ya bam bamta da ragowar wanda muke kawo muku a baya, domin kuwan nasan zaka bukaci amfani da wannan App din a halin yanzu ko kuma a nan gaba
Tunatarwa!!!
muna rokon yan uwa da suyi amfani da wannan Application din ta hanyar da ta dace, hanyar da bazaka cutar da wani ba ko wata da wannan Application din.
Babban Aikinsa
Babban aikin wannan App din zakaga wasu lokutan munje wani waje wanda aka hana daukar bidiyo ko sauti ko makamancin hakan, to da wannan APP din zaka iya daukar kowani bidiyo ko sauti batare da wani ya gani ko kuma ka daga wayarka, wani abun burgewa zaka iya bashi umarni kace duk minti daya ya daukar maka hoton wani waje a sirrance ko kuma sauti ba tare da anga ka kunna record ba a gaskiya wannan App din yana da abubuwa da yawa wanda kai da zaka dakko kai amfani dashi zaka gansu kuma ka koyi aiki dashi.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din.
wasalam, mun gode.