Yanda zaka hana wayarka ta dau zafi
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan Application din One booster.. hakika wannan Application din ya kamata ace kowa yanada shi a wayarsa musamman wanda Ram din wayarsu be kai sama da 8 ba saboda yana matukar taimakawa wajan rage shan caji da waya take yi.
sau dayawa muna samun korafin cewa "wayata tana daukar zafi sannan caji yana saurin daukewa" to dan uwa da yardar Allah wannan App din ze taimaka maka wajan hana dukkan wannan abubuwan ta hanyar yin amfani dashi saboda mafiya yawan mutane suna amfani da wayoyi masu Ram 2 zuwa 4 sannan suna saka Applications da yawa masu karfi da nauyi a wayarsu, to ta hanyar amfani da wannan insha Alla komai ze zo maka da sauki.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din.
wasalam, mun gode.