Da wannan App din zaka sai waya me kyau
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani.
Wannan wani Application ne?
Hakika wannan application ne wanda ya kamata a ce duk me amfani da wayar hannu yana dashi a wajansa ko nace a cikin wayarsa, kai har wanda be amfani da waya kamata yai a ce ma yana dashi
Babban aikin wannan App din
Kadan daga cikin aikin wannan App din ze baka damar yin wasu abubuwa na ban mamaki wanda bazakai zatonsu ba to wannan Application din ya ƙunshi dukkan wannan abubuwan da zan lissafo,wannan abun sune kamar haka
da wannan App din zaka san dukkan abunda ke faruwa a wayarka ko kuma wayarka take dashi kama daga su girman Ram, Gig, dukkan App din ciki da sauransu
wani abun burgewa a lokacin da kazo sayan waya gudun kada a cuceka zaka iya saka mata wannan App din kai tsaye zata nuna maka Bluetooth flash lighy Camera kuma ze baka damar ka gwada ka ga shin wannan abubuwan suna yi ko kuma bayayi batare da ka saya ba akan rashin sani, wannna shine kadan daga ayyukan wannan App din.
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din.
wasalam, mun gode.