Min menu

Pages

latest

Yanda zaka nemo wayar data bace ta hanyar (Tafi)

 

Yanda zaka nemo wayar data bace ta hanyar (Tafi)Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani.


Wannan wani Application ne? 


A cigaba da wannan channel take na kawo maku muhimman Application a yau munzo muku da wani babban Application wanda a aiki yana da girma da muhimmanci amma kuma a wajan koyo yana da saukin gaske.


Menene Babban aikin wannan App din?


A wasu lokutan mukan aje wayoyinmu a wani waje wanda mukan manta ko kuma muna zaune a dauke mana waya kuma muna jin kunyar muce a yi caje... wato binciken ina wayar take, a dan haka wannan App din ze taimaka mana wajan binciko inda wayar take ko kuma lalubo wanda ya dauka ta hanyar yi mata tafi da hannuwanka, hakika wannan App din yana da abun burgewa kuma beda nauyi kamar ragowar wasu Application din.Abun burgewa da wannan App din:


Bashida Nauyi

Baya amfani da Data

Kuma daga Playstore Yake
Idan kana san downloading dinsa 


Danna Nan 

Danna Nan 

Danna Nan 


Yanda zakayi downloading din wannan babban Application 


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din


Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .


Ina fatan zakuji dadin wannan Application din.


wasalam, mun gode.

reaction:

Comments