Yanda zaka ga abinda karamin danka ya keyi a wayarsa

Yanda zaka ga abinda karamin danka ya keyi a wayarsa

Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.

Wannan wani Application ne? 


sunan wannan App din ScreenTime, wannan Application din zai baka damar bibiyar danka ko matarka cikin sauki da kwanciyar hankali Dan haka na tabbata da wannan Application din zai taimaka muku sosai.

Screen Time, Application ne wanda zai baka sanin duk abinda danka ya keyi a wayarsa, kamar su chatting a whatsApp ko messenger ko Instagram da sauransu. Sannan wannan Application din zai na fada maka kowani irin searching da danka ya keyi, kamar a Google chrome ko Opera.
Kuma wannan Application din tsarkakakkene domin zakayi downloading dinsa ne a play store. 


Wannan zaka sa a wayar danka

Idan kana san downloading dinsa 

 Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Yanda zakayi downloading din wannan babban Application 


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din

Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .

Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum

wasalam, mun gode.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-