Yanda zaka bibiyi hakikanin wajan da mutum yake
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin.
Darasinmu na yau yana da matukar muhimmmanci domin haka munada bukatar yan uwa su tsaya su kalli wannan bidiyon a nitse kuma su karanta abinda muka fada.
Wannan wani Application/ web site?
Ayau ba Application bane domin kuwa wani web site ne da ze nuna maka duk inda mutum yake idan har kabishi yanda muka koya sannu a hankali.
A wasu lokutan mukan yarda wayoyinmu ko kuma a sace ko kuma mukan dinga neman masu laifi ko kuma zargin inda yaranmu suke tafiya ko kuma bincike inda mutum yake ta hanyar wasu Application din, ta yanda zakaga wataran akance sai mun biya kudi ko kuma kaga baya aiki yanda ya kamata, a don haka ne a yau zamu nuna wannan web site din da idan ka iya amfani dashi zaka share hawayanka na yawan tambayar da kake na Don Allah ya za ai na bibiyi wanda bama kusa dashi? kada in cikaku da surutu a wannan bidiyon zamu nuna wannan mashahurun website wanda idan har ka bi yanda muka koya to tabbas ( Zaka iya ganin duk inda mutum yake kuma zaka bibiya, wannan bidiyo yanada matukar muhimmanci ga kowa da kowa domin dole kanada bukatar sa kodai yau ko kuma wataran.
Mene amfanin wannan Website din?
1: Bibiyar duk wanda mukeso
2: Gano hakikanin inda mutum yake
3: Taimakawa jami'an tsaro wajan gano masu laifi
4: Kare kanka daga masu kidnapp
5: Saninsa ze kara wayar dakai
Idan kanasan shiga wannan website din
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Na tabbata da wannan Application din zai burge ku, kuma wannan Application din bashi da wuyar Amfani, acikin sauki zakayi amfani dashi.
Ina fatan zakuji dadin wannan Bidiyon,
Wassalamu Alaikum
Mungode.