Yanda zakai amfani da wayarka koda ta fashe
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin.
A yau darasinmu yanada matukar amfani domin yana iya shafarka ko kuma ya shafi waninka
Wannan wani Applicatio ne?
Hakika wannan Application ne da ya kamata ace kowa ya mallake shi domin kuwan ze taimaka maka a yayin faruwar wani tsautsayi da ze sami wayarko ko wayar waninka.
A sau da yawa mukan sami matsala ta fashewar waya ko Screen ko kuma wani abu ya sami fuskar waya ta yanda zakaga mutum bazai iya amfani da wani bangare na wayarsa ba, adon haka mukazo muku da wannan Application din da zai maida maka duk abinda yake cikin screen dinka tsakiya ta yanda zaka iya ganink komai a cikin wayaraka koda kuwan screen dinka ya sami matsala.
idan wannan Application din ya burgeka kuma kanasan sauke shi a kan wayarka:
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Na tabbata da wannan Application din zai burge ku, kuma wannan Application din bashi da wuyar Amfani, acikin sauki zakayi amfani dashi.
Ina fatan zakuji dadin wannan Bidiyon,
Wassalamu Alaikum
Mungode.