Yanda zakai chatting ba tare da ka kuna Data dinka ba

 Yanda zakai chatting ba tare da ka kuna Data dinka baAssalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.


Wannan wani Application ne?


Sunan wannan Babbabn App din( Bridgfy) wato daga jin sunan wannan App din kasan tabbas ya kamata kowa ya dauko shi.


Mene amfanin wannan Application din?


Babban aikin wannan App din shine ze baka damar yin magana wato chatting da yan uwa da abokan arziki cikin sauki kuma ba tare da ka bude Data ba ko an taba maka kudinka, ta hakane zamu samu damar yin duk abinda mukeso na magana da abokannmu, wani abun burgewa da wannan App din babu wani settings da zaka masa sosai ya fara aiki, kawai kai da abokanka kuna saka shi cikin wayarku zaku fara aiki dashi ba tare da bata lokaci ba.


Sannan abun burgewa kawai Bluetooth zaka kunnan kuyi connect shikenan kufara magana da abokanka na kusa


 Na tabbata da wannan Application din zai burge ku, kuma wannan Application din bashi da wuyar Amfani, acikin sauki zakayi amfani dashi.Idan kana san downloading dinsa 


Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan


 Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.


Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.


Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.


Yanda zakayi downloading din wannan babban Application 


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.


Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .


Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,

Wassalamu Alaikum

Mungode.

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-