Yanda zaka kara girman Memory na wayarka
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan App din SD maid hakika ya matukar burgeni duba da yanda ze baka damar yin Abu na musamman, bayan ka dakko wannan Application din Kai tsaye zaka fara Amfani dashi, wannan Application din bashi da nauyi kuma bashi da wahalar gane wa.
Amfaninsa
Wannan Application din zai baka damar goge duk wani Abu mara muhimmanci a wayarka, sannan zai dai-daita dukkanin Applications na wayarka, tahakanne zaka samu space mai dunbun yawa.
Zai goge maka duk wani duplicate Abu, misali idan kana da photos iri daya to wannan Application din zai goge su sai ya bar maka guda daya.
Dan haka zai burge ku sosai, domin zai amfane ku.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.