Yanda zaka karawa wayarka karfin Network
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan App din ForceLTE hakika ya matukar burgeni duba da yanda ze baka damar yin Abu na musamman, bayan ka dakko wannan Application din Kai tsaye zaka fara Amfani dashi, wannan Application din bashi da nauyi kuma bashi da wahalar gane wa.
Amfaninsa
Wannan Application din zai baka damar ka karawa wayarka Saurin Internet, idan wayarka 2G ne ko 3G ne to wannan Application din zai maida maka wayarka zuwa 4G mai karfi, ta yadda network din wayarka zaifi sauri sosai.
Bayan ka kunna wannan Application din zai da katar da dukkanin kiran da zai shiga a wayarka, dole sai ka kulle shi sannan kira zai fara zuwan maka.
Dan haka zai burge ku sosai, domin zai amfane ku.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.