Yanda zaka san sunan kowace waka da kaji
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.
Wannan wani Application ne?
wannan Application zai baka damar sanin duk wakar da kaji, zaka san sunanta da sunan mawakin da kuma inda zaka same ta.
Amfaninsa
Wannan Application din an kirkire shine domin yana taimakawa mutane domin kasan duk wakar da kake bukata, misali idan kana tafiya ko kuma kaje wani gurin kawai sai kaji waka, kuma wakar ta burge ka, to wannan Application din idan ka kunna shi zai fada maka sunan wannan wakar da sunan mawakin da kuma a'inda zaka iya samo wakar kamar youtube ko Spotify da sauransu.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.