Yanda zaka bawa wayarka umarni
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan lokacin
A darasinmu na yau zamu kawo muku bayanin wani Application wanda nasan ze matukar burge me karatu.
Bayanin App ɗin kai tsaye
A wani lokacin wani abu yakan faru damu mukasa danna wayoyinmu da hannayenmu ko irin ka taɓa ruwa ko hannunka beda kyau ko kuma wani abun daban wanda ze hanaka taɓa wayarka, a don haka mukazo da wannan App din wanda zaka dinga yimasa magana kai tsaye yana bude maka duk abinda kake so, misali: zaka iya cemasa " open WhatsApp" kai tsaye kaga ya buɗe shi a cikin wayarka, ko kuma kace ya daɗo maka volume ko kuma ya bude maka Video, abubuwa dai masu burgewa yakeyi
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Comments
Post a Comment