Yanda zaka kulle screen na wayarka
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application wanda nasan ze saku farin ciki a yayin amfani dashi.
Bayani wannan App din kai tsaye ze baka dama ne ka rufe ko kuma ka hana screen din wayarka motsi, a duk lokacin da ka kunna kallo, ko kuma ka saka wayarka a Aljihu kai tsaye wannan App din ze rufe maka screen din wayarka koda wani abu ya taɓa ta baze taɓu ba, ze bata kariya dada dannanwar da waya take maka akan rashin sani, ko kuma juyawar da take. domin ganin yadda wannan App din yake da kuma ƙarin bayaninsa zaka iya daukoshi zakafi fahimta da kyau
Nasan bayanina ba lalle ya gamshe ka ba sosai a don haka idan kana da bukatar É—auko wannan Application din zakaga wasu abubuwan da bamu bayyana ba.
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum