muhimman abubuwan da yakamata ace kowani matashi ya koya

Muhimman abubuwan da yakama ace kowani matashi ya koya


Assalamu alaikum warahmatullahi ƴan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin wanda kusan ya shafi kowa da kowa

Wannan wani darasi ne?

Kasancewar al'ummar mu ana musu nisa da kusan shekaru a harkar technology mukaga ya kamata a ce mun futo mun bayyana muku wasu muhimman abubuwa da yakama a ce tako wani hali ka koye su! kada kace " aini bana harkar computer, aini kasuwanci nakeyi don haka bazan tsaya koyon wannnan abun ba" to gaskiya wannan kuskure ne babba, domin nan gaba kaɗan zamani zeze wanda dukkan kasuwancin da zakai ko kuma aikin gwamnati ko na kamfani idan baka iya wannan abubuwan ba zaka zama ɗan kallo.kada in cika ku da surutu ya kamata ace na zayyano muku kaɗan daga muhimman abubuwan kamar haka...

1:  Graphic design

wannan yanada matuƙar muhimmanci a rayuwarmu ta tech, ta yanda zakaga muna ɗaukar maƙudan kudi muna bayarwa akan aimana zane zane domin tallata manhajojinmu ta hanyar wannan zanen a don haka yanzu akwai darussa da Apps wanda zasu iya koya maka wannan ta hanya mafi sauƙi, a wasu lokutan ma idan ka iya wannan bakada buƙatar seka nemi aikin gwamnati kawai zaka iya dinga yinsa ne seka saka online ka saida shi a dalolin kuɗi a don haka ynada matuƙar muhimmanci ace mun koye shi.

2: photography and videography

wannna hanya itace misali yanda mutum ze yi editin na hoto ya futa da haske da kala da kyau yanda ze burge kowa da kowa, yanzu wannan ya zama babbar sana'a ta yanda zakaga masu wannan sana'a suna mu'amala da manyan yan siyasa domin yi musu poster ta hotunan campaign ɗinsu, kuma wannan yana kawo kuɗi sosai shima, haka shima idan muka duba ɓangaran ɗaukar bidiyo zakaga mutum idan ya ƙware a wannan ɓangaran ana ɗaukarsa domin ɗakko bidiyoyin tallan kamfani, kayan kasuwa, harkar bloggin a YouTube, wajan manyan taruka... wanda wannan aiki ne wanda duk wanda ya koyeshi zefi kawo masa kuɗi fiye da aikin gwamnati.

3: Editing

Hakika mabiyanmu zasuyi sheda game da muhimmanci na editing ta yanda zakaga an ɗauki bidiyo akwai wuraren da yakamata a yanke ko a saka masa kala ko kuma a daɗa masa sauri ta yanda me kallo ze masa daɗin kallo sosai harma ya kalli bidiyon ka tun daga farko har ƙarshe, da wannan idan ka iya zaka iya aiki da masana'antu da dama ko kuma wasu mutane masu haɗa bidiyo, kasancewar babu wani bidiyo da zai futa babu editing, a don haka da wannan hanyar shima a na samu kudi sosai.


4: Social media management


Hakika wannan hanya ce wanda dukkan wannan hanyoyin  a cikinsu ta ɗan fisu sauƙi kuma zata fisu samun kuɗi idan ka ƙware, misalin wannan abun. Kasancewar manyan mutane da manyan kamfanunuwa basa iya motsi ba tare da Social media ba, zakaga suna neman masana wannan harkar domin biyansu ko nawa ne su dinga kular musu dashi, misali shuagaban ƙasa gwamna kamfanin Bua, Dan gote, duka sunada wanda suke kula musu da ɓangaran abunda ya shafi online, a don haka shima yanada matukar muhimmanci mu koya da kyau.

5: website development

daga ƙarshe itama wannan hanyar ta yanda zaka iya kula da website yanada matuƙar kyau a ce mutum ya koya domin idan ka ƙware kowani kamfani ze iya nemanka a kan kazo ka kular masa da website ɗinsa ta hanyar yi masa gyararraki, sanje sanje, tsara rubutu, saka kayayyaki, yin posting, da dai sauransu. A don haka shima wannna ilimi ne me zaman kansa sosai wanda ya kamata mu koya domin samun sana'a kuma mu kula da namu abubuwan.

Idan kana san kallon dukkan wannan darussan ka danna nan.. 

Na Farko


Na Biyu


Na Uku


NaHuɗu


Na Biyar

Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Kai tsaye kana dannawa zai kaika ainihin inda zakaga kuma ka koyi dukkan wannna darussan 


Ina fatan zakuji dadin wannan  muhimmin darasin


Wassalamu Alaikum

mun gode.

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-