yanda zaka gane waya me gyara a cikinta
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin.
Yaya wannan App ɗin yake?
Haƙika wannan App ne wanda ya kamata ko baka ɗakko shiba ace ka sanshi kuma kasan yanda ake amfani dashi duba da yanda yake da muhimmanci a wajanmu, wato mu masu amfani da sayen wayoyin Android.
A wasu lokutan mukan sayi wayoyin hannu bayan mun koma gida sai mu samesu da matsala wataran kaga speaker batayi ko kuma screen ya lalace bayayi sosai ko kuma wasu ɓoyayyun matsala dai wanda sai daga baya suke futowa, Adon haka wannan App ɗin ze bunciko maka wannan matsalar da zaran akwaita a cikin wayarka daka saya.
Wasu daga manyan matsaloli da yake nunawa
1. flash
2. face id
3. vibration
4. Gps
5. Battery temperature
6. sensor
7. LCD
8. multi touch
9. speaker
10. power button
Bayan ka koyi amfani da wannan App ɗin, zaka iya gano kowace matsala a cikin wayarka kafin ciniki ya faɗa, don gudun samun matsala
Idan kana san download ɗin wannan App ɗin...
Ina fatan zakuji daɗi amfani da wannan App din
Wassalamu Alaikum, mun gode
Comments
Post a Comment