yanda zaka haɗa bidiyo a kowani platform me kyau
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan lokacin.
A yau bidiyonmu ya shafi dukkan wani me amfani da platform, wato idan mukace platform muna nufin a dukkan wasu masu amfani da facebook, Instagram, twitter, TicToc da sauransu. A sau da yawa zakaga wataran munasan haɗa hotunanmu kuma mu saka masa sautin da muke so, sannan zamuso mu jera shi ya dinga tafiya daga wannan se wannan ya shiga cikin burgewa da raba murayar sauti.
Adon haka muka zo muku da wannan App ɗin wanda ze baka damar haɗa dukkan wani bidiyo wanda zaka iya saka hotunan ka kuma ka iya saka shi a kowani platform ya hau yayi kyau, kama daga haɗa bidiyon Siyaysa, aure, Birthday, waleema da dai sauransu.
Idan kana san downloading dinsa ga masu Iphone
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum