yanda zaka ragewa kowani bidiyo nauyi

 yanda zaka ragewa kowanni bidiyo nauyi







Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan lokacin.


A yau darasinmu ze nuna mana wani Application wanda ze baka dama ka rage nauyin kowanni bidiyo bayan an daukeshi.


Wani irin App ne wannan?


Wannan Application ne wanda ya jima ana amfani dashi kuma mutane da dama suna jin daÉ—insa, a don haka mukazo muku dashi, domin mun san mabiya suna yawan É—aukar bidiyo a wayarsu ta hannu kuma suna san barinsa amma sakamakon nauyin da bidiyon Camera yake dashi yakan damu wayarka har takai ga seka goge wannan bidiyon dukda kana sanshi, adon haka muka kawo muku wannan App É—in wanda ze baka dama ka rage bidiyonka misali daga MB 900 izuwa MB 90 ko 200 ko 300 duk dai yanda kake so clear É—insa ta kasance, sai dai cewa idan ka cire MB É—insa da yawa to Clear É—insa ze ragu da yawa, iya dai yanda kake so.


Manyan abun burgewa a wannan App É—in


1: beda nauyi a waya kuma beda wahalar koya


2: Babu tallace tallace masu takura


3: daga Playstor yake kuma beda nauyi


4: baya amfani da network ko Data


5:zaka iya rage ko MB nawa kake so


Idan kana san downloading dinsa ga masu (Android)


Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan


Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Yanda zakayi downloading din wannan babban Application 


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din


Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .


Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,


Wassalamu Alaikum


Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-