yanda zaka rufe kowani kira na wayarka

yanda zaka rufe kowani kira na wayarka 


Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan darasin.

wannan wani App ne?

wannan Application ne wanda muka jima munasan nunawa mutane,amma lokacin nuna shi bezo ba sai yanzu, wannan Application ɗin a taƙaice yana bayanine a kan abinda ya danganci kirana waya.

Bayanin wannan App ɗin

wannan App ɗin kai tsaye yana bayanine akan wani lokacin idan aka kiraka a waya kai tsaye kuma bata hannunka tana hannun wani ko wata wadda bakasan aga wannan number da ta shigo cikin wayarka saboda yanayi na tsaro ko makamancin hakan, to zaka iya rufewa kiran ze shigo amma babu wanda ze iya gani ko ɗaga wayar har sai kazo ka saka code ko kuma pattern.

Idan kana san download ɗin wannan App ɗin...

Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan


Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

yanda zaka sauke wannnan Apps ɗin

Da zaran ka dannan zekaika inda zaka ɗakko wannan App ɗin se yace dakai install kana dannan install ze fara tafiya sannan ya sauka a wayarka.

Ina  fatan zakuji daɗi amfani da wannan App din.

Wassalamu Alaikum, mun gode 

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-