Ana yawan ƙarya da wannan App ɗin
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan lokacin.
A darasinmu na wannan lokaci zamu nuna wani Application wanda ze sanar dakai yanda ake kiran wayar bogi.
Wani irin App ne wannan?
A wannan Application ɗin zamu koyi yanda zaka gane ko kuma kayi ko ka tsokani abokinka ta hanyar kiran bogi. Sau dayawa zakuga cewa ana amfani da irin wannan Application ɗin wajan yiwa mutane sharri ko kuma abubuwa n da basuyi ba, sannan kaga anata yaɗawa saboda a kafa hujja dasu. Adon haka muka zaƙulo ɗaya daga cikin wannan App ɗin domin yin bayaninsa a taƙaice.
Bayanin App ɗin a taƙaice
Da fari dai wannan App ɗin beda nauyi kuma ba'a amfani dashi da Data ko MB, a don haka ana amfani da wannan App ɗin wajan ƙirƙiro number ƙarya, domin sannan ka saita dai dai lokacin da kakeso wannan kiran ya shigo, kai harma da saka irin maganar da kakeso na kusa dakai yaji,kuma wani abun burgewa wajan koyan wannan App ɗin a fili yake domin komai yanada sauki ta yanda cikin dannawa kaɗan zaka gane yanda ake amfani dashi.
A don haka muna fatan ƴan uwa suyi amfani da wannan App ɗin ta hanyar da ta dace kada a cutar da mutum.
Idan kanasan downloading wannan App ɗin danna nan.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum, mun gode.