Application guda ɗaya me abubuwan burgewa biyar(5)
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan darasin.
Wannan wani App ne?
Haƙiƙa wannan Application ne wanda an haɗa abubuwa na Editing kusan guda biyar acikinsa shi kaɗai, nasan me karatu zece wannan wasu abububaa ne har guda biyar masu amfani ga editing? A don haka zamu shiga bayanin waɗannan abubuwa guda biyara a taƙaice.
ABU NA FARKO( CANZA LAUNIN KAYA)
a wannan App ɗin duk kayan da ka saka idan fari ne ko baƙi ko ja zaka iya sauyashi daga wannan kalar izuwa wannan kalar, wato daga baƙar riga ko kuma koriya izuwa kalar ruwan ɗorawa.
ABU NA BIYU(ƘARAWA HOTO CLEAR)
Wataran zakaga an ɗauki hoto beda clear ko baida haske to a wannan App ɗin cikin dannawa biyu zaka gyara haske da clear hotonka.
NA UKU( CIRE ABUNDA BAKASAN YA FUTO A HOTONKA)
A wasu lokutan mukan ɗauki hoto kaga wani Mutum ko wani abu ya futo a cikin hoton wanda munasan mu goge shi to shima a wannan a pp ɗin zaka iya danna gogewa cikin yanayi me kyau kuma kaga ya gogu a nan take ya futa daga hoton.
NA HUƊU( CANZA KALAR SARARIN SAMA)
A wannan App ɗin idan ka ɗau hoto sama ta futo zaka iya sanjawa izuwa kalar hadari kamar za ai ruwa, ko kuma kamar rana zata faɗi ko kuma gajimare masu kyau sosai.
NA BIYAR(CANZA BANGON HOTO)
A wasu lokutan zakaga mun ɗauki hoto Background ɗin baida kyawun gani ko kuma munasan saka wanda yafi wancan kyau, a don haka zamu iya canzawa a cikin wannan App ɗi ta hanya mafi sauƙi.
Idan kana san download ďin wannan App
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Da zaran ka dannan zekaika inda zaka ɗakko wannan App ɗin se yace dakai install kana dannan install ze fara tafiya sannan ya sauka a wayarka.
Ina fatan zakuji daɗi amfani da wannan App din
Wassalamu Alaikum, mun gode