yanda zaka ciro bidiyo a cikin kowanni film
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Wannan wani Application ne?
Wannan App ne wanda ya kamata ace ka sakashi a cikin wayarka saboda abubuwan da zasu iya faruwa nan gaba na buƙatarsa ta gaggawa,ya kamata ace ka barshi a wayarka saboda sauƙin amfani dashi da kuma rashin damun waya da ba yayi.
Mene amfanin wannan Application din?
Wata rana zakaga wani dogon bidiyo a wayarka ko kuma film, to a cikinsa akwai wani waje da kake buƙatar kaga ka yankoshi wanda ta yiwu yakai minti 1 ko sakwan 10 wanda ze iya baka dama ka saka a story ɗinka na WhatsApp ko Instagram ko Facebook, a don haka da wannan App ɗin zaka iya amfani domin ka yanke kowani sakwan a cikin bidiyo kuma kayi amfani dashi a duk inda kake so.
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.