Jerin Applications (2) mafi kyau a wannan watan(TC slim)
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan darasin.
A darasinmu na yau munzo da wani Application wanda ya kamata ace kowa ya sauke shi,domin idan bakai amfani dashi yanzu ba zakai amfani dashi nan gaba.
Bayanin APPLICATION ɗin a takaice
A wasu lokutan wasu mukanso mu buɗe Data na wayarmu domin yin wani Amfanin wanda bamasan saƙonnin WhatsApp su shigo ko kuma abokanmu su ganmu online, ko kuma wataran ma idan wani abokinka yana ɗaukar maka waya ya shiga YouTube duk dai da wannan App ɗin zaka iya kashe datar iya YouTube ko WhatsApp ko wani App ma.. yaƙi yi har saika koma ka buɗe shi sannan ze dawo aiko.
Hanyar amfani dashi
kawai idan ka danna cikinsa zakaga jerin dukkan App ɗin wayarka, kawai bayan ka kunna madannin sama, se kazo kan App ɗin da kake son rufe data ɗinsa seka danna shi, kawai zakaga ya canza kala shikenan zaka iya buɗe datar wayarka, ba tare da saƙonni sun shigo a wannan App ɗin ba.
Haƙika nasan ze matuƙar burge masu karatu domin yanada wasu abubuwan wanda bama zan iya lissafo su ba, idan ka sauke duka zakaci karo dasu, musamman yanda fuskar wannan App ɗin tanada sauƙin koya sannan batada yawa ko kaɗan.
Idan kana san downloading ɗi wannan App ɗin
Ina fatan zakuji daɗi amfani da wannan App din
Wassalamu Alaikum,
mun gode
Comments
Post a Comment