Sabbin Applications (3) a Google Playstor,kada ka bari a cuce ka dana ƙarshe
Assalamu alaikum warahmatullahi, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin.
(Application na farko)
Easy uninstaller
Haƙiƙa wannan App ɗin yanada kyau da sauƙaƙawar da yakamata mu barshi a wayarmu,saboda ze bamu dama mu iya goge dukkan Application ɗinmu wanda suka cike mana waya a lokaci guda kuma cikin sauƙi,sannan gogewa ta yanda baze dawo ba.
Domin sauke wannnan App ɗin...
(Application NA BIYU)
Quote Lab
APPLICATION ɗinmu na biyu ze baka dama ne kayi duk rubutun da kake buƙata a cikin screen ɗin wayarkan,ta hanyar canza masa launi da girma sannan kuma da duk background ɗin da kake so ka saka. wani lokacin mukanga wasu maganganu wanda zasu burge mu, munasan mu haddace su ko kuma mu saka su a screen ɗin wayarmu amma bazamu iya ba, to wannan App ɗin ze baka dama ka saka kowani rubutu a screen na wayarka,sannan kuma ba iya wannan ba ma domin har story na dukkan platforms ze baka damar ka haɗa hoto ko wata magana kuma ka saka shi a nan take.
Idan kanasan Downloading wannan App ɗin ...
Application na (uku)
Edit web page
A sau dayawa matasan zamani idan musu ya rikice a kance a tafi a duba Google, to ɗan uwa shin kasan da wannan App ɗi zaka iya Editing kowani Result da Google ya baka domi tsokanar abokanka, a don haka a bi a hankali sannan kuma a san wannan App ɗi domin bakomai za'a nuna mana a Google ba kuma mu yarda, har se mun tabbatar, domin ko result ɗin wasa da komai kana iya shiga Google ka canza da wannan App ɗin
idan kanasan Downloading ɗinsa...
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakai install, bayan ka danna inda mukace Danna Nan kai tsaye ze kaika Playstor daga nan zakaga ansaka Install seka danna kai tsaye ze sauka a kan wayarka.
Duka dai anan darasin namu ze dasa aya dafatan wannan bayanin ya gamsar daku yan uwa.
Wasalam mun gode.