Facebook video
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan darasin.
A darasinmu na yau munzo da wani Application wanda ta yiwu kayi amfani dashi ta hanyoyi da yawa.
Bayanin APPLICATION É—in a takaice
A baya mun kawo ire iren wannan App ɗin sedai ba lallai ya cigaba dayi ba.Kai koda ma yaci gaba dayi to wannan wanda zamuyi bayani a taƙaice yafishi kyau da kuma sauƙin amfani..,domin kuwa beda nauyi kwata kwata.
Hanyar amfani dashi
Bayan ka buɗeshi kamar yanda muka nuna a bidiyonka tsaye ze nuna maka fuska guda 1 wadda tanada matuƙar sauƙi, wannan fuskar itace bayan kayo Copy ɗin link ɗinka,so dayawa kana shiga App ɗin zakaga ya fara maka searching sedai kawai ka danna wata kibiya ta alamar download, zakaga a ƙasa ya nuna maka yawan MB ɗin sanna kawai cikin minti kaɗan kaga ya sauke maka wannan bidiyo
Haƙika nasan ze matuƙar burge masu karatu domin yanada wasu abubuwan wanda bama zan iya lissafo su ba, idan ka sauke duka zakaci karo dasu, musamman yanda fuskar wannan App ɗin tanada sauƙin koya sannan batada yawa ko kaɗan.
Idan kana san downloading É—in wannan App É—in
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Ina fatan zakuji daÉ—in amfani da wannan App din
Wassalamu Alaikum,
mun gode.