Yanda zaka haɗa invitation Card cikin minti 3 a wayarka Yanda zaka haɗa invitation Card cikin minti 3 a wayarka 


Assalamu alaikum warahmatullahi, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan sabon bidiyon.


A cigaba da kawo muku muhimman Applications na wayar Android da wannan channel take a yau munzo muku da wani babban Application wanda idan ka sakashi a wayarka ze matuƙar temaka mata.

WANNAN WACE MANHAJA CE?

A sau da yawa akan turo mana katin gayyatar buki ko sauka ko suna ko wani taro makamancin haka, ta yanda zakaga anrubuta shi a bidiyo ɗan ƙarami,wanda zakaga ya burge mutane, kuma suna iya samun damar yin story da wannan bidiyon.To wannan manhajar zata taimaka maka wajan yin dukkan abunda na lissafo cikin sauƙi bama iya shiba harda wani abun dabam wanda ze matuƙar burgeka.


ABUBUWAN DA WANNAN MANHAJA YAZO DASHI

Wannan manhaja zata baka dama ka saka hotonka da kuma background music na aure duk wanda kake so,sannan kuma da Amination, sannan zaka iya searching a cikin wannan App ɗin na ƙarin wasu abubuwa na burgewa da zaka ƙawata invitation Card ɗinka, abin burgewa yanda ake nuna hannu yana rubutu da kuma yanda zaka saka music ya kuma hau.


Idan kanasan downloading wannan App ɗin 

Danna nan

Danna nan

Danna nan

Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Yanda zakai install, bayan ka danna inda mukace Danna Nan kai tsaye ze kaika Playstor daga nan zakaga ansaka Install seka danna kai tsaye ze sauka a kan wayarka.


Duka dai anan darasin namu ze dasa aya dafatan wannan bayanin ya gamsar daku yan uwa.

Wasalam mun gode.

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-