Yanda zaka bawa budurwarka wayarka ba tare da tsoro ba.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu, musamman wadanda suke aje abubuwan sirri a wayarsu.
Wannan wani Application ne
Sunansa Ultra Lock wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, kaima kar ka bari a barka a baya, domin yanada matukar amfani.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din zai taimaka maka gurin kare wayarka daga masu bincike a wayar da ba tasu ba, saboda akwai mutane da yawa wanda burinsu su dau wayar wasu suyi musu bincike.
Wannan Application din zai baka damar sakawa duk Application din da kake so security, kuma security mai canja kansa, wanda kaika daine ka isa ka cire shi.
Na tabbata da wannan Application din zai burge ku, kuma wannan Application din bashi da wuyar Amfani, acikin sauki zakayi amfani dashi, kuma zaka sameshi a play store.
Idan kana san downloading dinsa A play store
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.