Hanyar da zaka maida wayarka ta Android ta koma kamar Iphone

 Hanyar da zaka maida wayarka ta Android ta koma kamar IphoneAssalamu alaikum warahmatullahi, yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan sabon bidiyon.


Idan kanaso kayi wannan abun to dole kana bukatar Applications 4, dan haka zanyi muku bayaninsu dalla-dalla kuma a takaice.


Walp AppWannan Application din zai taimaka muku sosai, domin shine zai Baku damar canja wallpaper wayarku zuwa ta IPhone, kuma wani abun burgewa Application din bashida nauyi kwata-kwata acikin yan seconni zaku dakko shi. Sannan yana da saukin fahimta.


Idan kana bukatar dakko shi


Danna Nan 

Danna Nan 

Danna Nan 


Volume style AppKai daga jin sunan wannan Application din kasan aikin da zaiyi, a takwaice wannan Application din zai canja gurin volume na wayarku ya maida shi zuwa ta IPhone, kuma a wannan Application din ba iya iphone kadai zai baka dama ba, zai baka damar canja duk kalar da kake bukata. Na tabbata da wannan Application din zai burge mutane da yawa.


Idan kana bukatar dakko shi


Danna Nan 

Danna Nan 

Danna Nan 


Icontrol and inoty iosDukkanin mu mun san Iphone tana da Notifications nata na daban, toh dan haka idan kana bukatar kaima na wayarka ya zama kamar na Android to kayi amfani da wannan Application din, domin zai magance maka wannan matsalar.


Idan kana bukatar dakko shi


Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan


True phone App


Wannan Application din zai baka damar canja gurin kiranka, ta yadda daga an kiraka zai zo maka kamar na iphone, dan haka wannan ma zai burge ku


Domin dakko shi


Danna Nan 

Danna Nan 

Danna Nan 


Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Yanda zakayi downloading din wadannan Applications din


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.


Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .


Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,

Wassalamu Alaikum

Mungode.

CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-