Hanyoyin da akafi samun kudi a Internet a wannnan lokacin

 Hanyoyin da akafi samun kudi a Internet a wannnan lokacin
Kamar yadda kowa yasani, a wannan lokacin dubban mutane suna samun makudan kudade a Internet a wannan zamanin, dan haka nazo mu tattauna akan wasu daga ciki, domin zasu taimaka mana gurin rage bukatunmu na yau da gobe.


A wannan post din bazanyi magana akan youtube ko website ba, domin nayi bayaninsu a baya, dan haka wanda yake bukatarsu sai ya duba posts dinmu na baya.


Wannan sirin zaina zuwa muku a cikin wannan matan mai Albarka, Ramadan. 1. Facebook & Instagram Ads 


Wannan hanya ce da ake samun kudi sosai, ta hanyar koyan tallata abu a Facebook ko Instagram, misali, dukkaninmu munsan Ana tallata abubuwa a wadannan kafa, kuma mutanenmu basuda ishashen ilimi akan abun, dan haka kai zakaje ka koyo yadda ake bawa Facebook da Instagram talla, domin kanayiwa mutane suna biyaka. Idan Facebook sukace zasu nunawa mutum 1,000 akan nera 100 kai kuma sai Dora ribarka akan haka, misali duk mutum 1,000 zaka amshi 120, kaga ka samu nera ishirin a duk dubu daya. Wannan karamin misali nayi maka.


Kuma zaka iya bude aji (classes) domin koyawa mutane wannan sirrin na tallata kaya a Facebook da Instagram, sai ka sanya farashin da yayi dai-dai da kai.

Misali akan yadda mutane suke tallata darasin wannan Domin koyon Facebook & Instagram Ads 

For English 

pour le fran├žais

Amazon KDP


Wannan hanyace ta samun kudi a Internet ta haryar saida littatafai (Books) koda kuwa kai ba marubuci bane, karka damu zanyi maka bayani dalla-dalla.


Amazon KDP yana ba da damar buga littattafan e-books, takardu, da hardcover books a kyauta. Zasu baka damar daura littatafai acikin Amazon, Ana samun kudi sosai.


Idan Allah ya kaimu gobe zanzo muku da cikakken bayanai akan Amazon KDP. Dan haka muna fatan zaku kasance damu.

Mungode.

Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-