Manyan Applications 3 masu Muhimmanci
Assalamu alaikum warahmatullah, Æ´an uwan barkanmu da sake saduwa a wannan sabon bidiyon wanda yake na musamman a wannan channel taku me albarka.
Wanda a wannan bidiyon zamuyi bayanin wasu muhimman Applications guda 3 wanda tabbas zasu burge duk wanda yake karanta wannan rubutu.
Wannan wani Application ne na (Farko)?
(File commander managar)
Bayanin App na farko kai tsaye (1)
Babban aikin wannan App ɗin wani lokacin zakaga wayarka ka ajiye wasu abubuwa na sirri wanda bazakaso a gansu a Gallery ɗinka ba, amma kuma kanasan su zauna a wayarka a don haka wannan App ɗin ze taimaka maka wajan ɓoyewa.Sannan wani abun burgewa zaka iya saka masa Security ka rufe shi wanda babu wani mutum da ze iya buɗe maka ya gani har se ka saka wannan Security ɗin sannan ze buɗe.
Abinda ya fi jan hankalina da wannan App ɗin idan kana fama da ƙaramcin Space ko Storage na wayarka beda girma zaka iya ƙarawa domin ka ɓoye wani bidiyo ko sauti me nauyin gaske, tabbas yazo da wasu abubuwan da lokaci baze bamu dama muyi bayaninsu ba.
idan kanasa downloading wannan na Farkon
Mene amfanin App na (Biyu)?
Sunansa Goaly alhabit....(Wow)
Haƙiƙa wannan App ɗin ya kamata ace kowa ya sauke shi domin ganin yanda akai amfani da technology me bada mamaki.
Sau da yawa zakaga inasan yin wani al'amura na yau da kullum amma zakaga abubuwa sunzo sunyi mini yawa nakan manta wasu muhimman abubuwa wanda dasune zan gudanar da rayuwa ta cikin tsari da kuma cika alaƙawari.
A don haka wannan App ɗin zaka iya amfani dashi wajan tsara dukkan wasu abubuwan da zakai daga yau zuwa dare ze dinga sanar dakai da zaran lokaci yayi kuma ya sanar dakai ga abunda kace zakai, kai harma daga yau zuwa sati guda ko sama da haka zaka iya tsarawa... ya salam! gaskiya wannan manhaja ta matuƙar burgeni sosai.
Idan kana san downloading dinsa
Wani irine App É—inmu na( 3)
A kullum mukan ɗauki bidiyo ko kuma a tura mana bidiyo, a bune sananne bidiyon Camera yana da matuƙar nauyi, wato wanda aka ɗauka kai tsaye.
A don haka wannan App É—i ze baka dama ka ragewa ko wani bidiyo nauyi batare da Clear É—insa ya ragu ba, ta yanda zaka iya turawa wani shima ya tura maka, sannan ka sa ka a Story na WhatsApp da facebook da sauransu, wani abun burgewa da waÉ—annan App É—in basa Amfani da Data kyauta ne sosai.
idan kanasan downloading wannan Game É—in
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.