Zaka iya amfani da WhatsApp guda a wayoyi (4) rigis

 Zaka iya amfani da WhatsApp guda a wayoyi (4) rigis






Shin wannan sabon abun da WhatsApp yazo dashi ci gaba ne ko kuma ze haifar da Matsala?


A yammacin yau ne shahararren me kuÉ—in nan wato mammalakin WhatsApp da facebook wato Marc Zuckerberg ya sanar da damar yin amfani da WhatsApp a cikin adadin wayoyi dabam dabam har guda (4) rigis.


Shin me karatu ya kaga hakan?

Kasancewar cigaban da ake samu a duniya na komai da kuma sawwaƙa abubuwa da ake musamman a fannin Technology ya saka kamfanin WhatsApp ya kawo wannan abun wanda ze sauƙaƙawa me amfani wajan yin amfani dashi manhajar ta WhatsApp a cikin sauƙi a wayoyin dabam dabam, da kuma lambarka guda ɗaya,wanda tuni ya jima yana shirin sanar da wannan cigaban wanda a ranar yau ya tabbatar da hakan.

Wannan abun ya matuƙar burge wasu mutane wanda suke da wayoyi sana da guda ɗaya kuma suke kasuwanci dasu,sannan ze sauƙaƙa wajan abubuwa da yawa wanda nasan se angwada za'a gano babban amfani wannan cigaban da WhatsApp ya kawo.


Sedai ni a nawa ra'ayin ina ganin anya hacking É—in Account na Whatsapp baze yawa ba?

Daga baya kuma na tuna ai WhatsApp baze kawo wannan kai tsaye ba, batare da ya kula da hakan ba.

A don haka É—an uwa idan ka karanta wannan rubutun me kake gani game da wannan sabon abun da WhatsApp yazo dashi?

Shin Satar account zatai yawa?

ko kuma wannan cigaba yayi maka sosai, muna jiran ra'ayinku a ƙasan Comments.


Wa salam mun gode.

Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-