Hanyar da zaka sayi kaya masu sauki a china

 Hanyar da zaka sayi kaya masu sauki a china

Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake kasan cewa daku a wannan saban darasin, a darasinmu na yau zanyi muku bayani ne akan Hanyar da zaka siyi duk kalan kayan da kake kuma a kowace kasa, misali China, Turkeye, Bangladash da sauransu.

Da farko zan fara yi mana bayani akan Hanyoyi ingantattu wanda zaku iya siyan kaya cikin sauki, kuma sukawo maka har Nigeria. akwai irinsu womata, cavamall da sauransu, zan yi mana karamin bayani akan cavamall.

Cavamall


kamfanine wanda suke da warehouse a china, kuma na yan china ne, sannan suna da warehouse a lagos da ibadan da kano, zaka iya siyan kaya masu sauki sosai sannan su kawo maka har kano acikin kwana 10 zuwa 12. Idan ka samu matsala zakaje gunsu kai katsaye domin korafi akan matsalarka.

Domin downloading dinsaBayan wadannan wadanda suke da warehouse a Nigeria akwai manya-manya, kamar su AliExpress, Alibaba da 1688 da sauransu. Mutum zai iya siyan kaya anan ba tare da fargaba sosai ba, Amma matsalar da muke fama da ita, itace da payment online.

Dan haka na kawo mana hanya mai sauki domin siyan duk abinda kake online koda katuna (Banks) na Nigeria basa aiki.

Na farko


Payday Application ne wanda zai baka damar samun master card na dollar, to idan ka mallake shi zaka iya siyan duk abinda kake bukata, kuma bashida wahalar amfani, sannan zaka sameshi a play store.

Domin downloading dinsaNa Biyu


Chipper cash shima wannan  Application ne wanda zai baka damar samun master card na dollar, to idan ka mallake shi zaka iya siyan duk abinda kake bukata, kuma bashida wahalar amfani, amma payday yana finsa sauki gurin Exchanging Naira zuwa dollar sannan zaka sameshi a play store.

Domin downloading dinsa

A wani bangaren ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Mungode.


CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-