Hanyoyin da ake kallon kafa

Hanyoyin da ake kallon kafa 


Assalamu alaikum, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi magana ne akan hanyoyin da zaku iya kallan kwallon kafa a wayoyinku ta hanyar amfani da website ko kuma Applications. Dan haka ka kasance damu har karshe domin zamuyi muku bayani dalla-dalla da yardar Allah.

Ta hanyar Website


Akwai website masu matukar yawa wadanda zasu baku damar kallon ball a wayoyinku, kuma network kawai kake bukata, zasu taimaka maka gurin tattala storage na wayarka, domin bzaka dakko Application ba idan zakayi amfani dasu.

Website din da nayi bayani akansa shine akwai irinsu koora live English, Live soccer Tv da sauransu, kuma suna da saukin mu'amala.


Ta hanyar Applications

shima ta Hanyar Applications akwai su da yawa sosai, kuma basu da nauyi domin basafin 10 to 20 MB dan haka acikin ruwan sanyi zakayi downloading dinsu, ni nafi amfani da yaccine domin akowani lokaci sunayin updating din Application din, kuma daga sun sami matsala suke kokari suyi maganinta. Suna notification a duk lokacin da za'a fara wasa ko kuma lokacin da za'a dawo daga hutun rabin lokaci.

Domin downloading dinsaKuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Mungode.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-