YANDA ZAKA RABA SCREEN ƊIN WAYARKA BIYU(2)

 

YANDA ZAKA RABA SCREEN ƊIN WAYARKA BIYU(2)


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci sannan kuma barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin.

A cigaba da kawo muku muhimman Applications da wannan Channel takeyi a yau munzo muku da wasu Application wanda mun tabbata da zasu burgeku za kuma su ƙayatar daku,domin muma mun ɗakko su munyi amfani dasu kuma muna kan yin amfani dasu domi morewa wayarmu ta Android.

MENENE DALILIN KAWO WANNAN APP ƊIN?


sua da yawa zaka sami ma'abota amfani da waya suna yawan yin ayyuka da ita akai akai ta yanda zakaga, abubuwa sun haɗe maka a lokaci guda kanasan yin wannan aikin sannan kuma wani ya kunno kai. Ko kuma a wasu lokutan zakaga munasan koyon abu amma da zaran mun gama kallan wanna abun da muka koya wajan kwatanta shi se kaga mun manta, wanda wannan yana saka mu muje mu ƙara kallan wanna bidiyon. Wannan yana haifar mana da wahala sannan yana ɓata mana lokaci. A don haka mukazo da wannan App ɗin domin ya sauƙaƙa maka dukkan wannan wahalhalun.

(BAYANIN APP NA FARKO A TAƘAICE)


A wasu lokutan ayyuka sukan haɗe mana kuma duk a cikin wayarmu wanda zakaga mun buƙaci muyi sauri mu gudanar da wannan aikin a lokaci guda.
Ko kuma a wasu lokutan mukan shiga YouTube domin koyon wani abun,ko kuma mukan kunna wani bidiyon domin kallansa,sannan mu koyi wani abun.

To wannan APPLICATIONS ɗin ze baka dama ka raba Screen ɗin wayarka domin yin abu biyu a lokaci guda. Wato Misali a sama kana kallan YouTube a ƙasa kuma kana kwatanta abinda kake koya.

Ko a wani lokacin ma zakaga kanasan koyon karatun Alkur'ani mai girma,to wannan App ɗin shima ze taimaka maka ta hanyar jin sautin karatun a YouTube ko wani wajan, a gefe guda kuma kana kallan App ɗin Qur'anin . Haka dai zaka samu damar yiwa kowani APP a wayarka wannan abun me matuƙar burgewa.

YAYA AKE AMFANI DA WANNAN APP ƊIN?


Kawai zaka shiga cikin App ɗinka, bayan ka sauke shi a cikin wayarka, kana buɗewa ze nuna maka wani rubutu a can ƙasa inda aka rubuta Shortcut da yaran Hausa. Kana dannawa ze sake kaika wani shafin da zakaga zaɓi guda biyu, wanda suka haɗa da (Top App da kuma Bottom App) .

Da farko zaka dannan Top App shine ze baka damar ka saka duk App ɗin da kake buƙata ya kasance a sama wayarka yayi da ka raba Screen ɗin.

Shi kuma Bottom App shine wanda ze kasance a ƙasa,wato wanda ze baka dama ka saka duk App ɗin da yake a Ƙasan Screen ɗin wayarka yayin da ka raba Screen ɗin.

Bayan ka gama dannawa kawai seka danna Save daga gefen hannunka na dama a ƙasa. Shikenan kana futa zakaga ya ƙaru a cikin wayarka tamkar yanda su WhatsApp suke shima kamar wani App.
Haka ma idan kanasan ƙara wani abun duka dai hakan zakai.

Idana kanasan downloading wannan App ɗin ka..


DANNA NAN
DANNA NAN
DANNA NAN


APPLICATION NA BIYU ME SUNA(REMOVE VG)


Wannan Manhaja yana ɗaya daga cikin manhajojin da sama da miliyoyin mutane suka ɗakko suna amfani da ita saboda amfani da sauƙi da kuma ingancinta sannan da rashin nauyi a kana wayarka.

DALILIN KAWO WANNAN APP ƊIN


Sau da yawa zakaga samari da ƴan mata da ƴan kasuwa suna ƙoƙarin ɗaukar hoton kayansu na sayarwa domin tallatawa izuwa groups ko kuma Platforms da muke dasu domin ya ɗauki hankali masu saya, sedai zakaga da yawa basa iya samun Background me kyau wanda ze basu damar wannan ɗaukar da suke san suyi. Ko kuma ma zakaga sun ɗauka amma abun haushi zakaga inda aka ɗauka be da kyawun da zeja hankalin masu saya. Adon haka mukazo da wannan App wanda a cikin sauƙi zakai dukkan wannan ayyukan naka sannan ka saka duk kalar Background ɗin da kake so.

Ba iya nan ba ma, a wani lokacin zakaga mu dakanmu mun ɗauki hoto a waje mara kyau, ko kuma muna san gyara Background ɗin da muke so ko kuma watarn zakaga a profile ɗinmu na kowani Platforms munasan canza masa kala izuwa baƙi ko dai wata kalar dabam. To duk wannan App ɗin ze baka dama kai wannanan abun, wannan shine babban dalilin kawo maku domin jin daɗinku

MENENE BABBAN AIKINTA?


Wannan App ze baka damar yayin da kai hoto na wasu kayayyaki na sayarwa ko kuma wani hoton abun wanda zakaga sau da yawa idan kayan sayarwa ne kana buƙatar ya zama me ɗaukar ido ta hanyar gyara shi da saka masa Background me kyau, ta yiwu ko Baƙi ko fari ko shuɗi ko wacce kalar dai da kake so, to wannan App ɗi ze baka dama kai dukkan abunda kake buƙata me kama da haka.

YAYA ZANYI AMFANI DA WANNAN APP?


Da farko ka tabbatar ka buɗe Data ɗinka dukda be ɗaukar Data me yawa, kana buɗewa, fuska ta farko da ze kawo maka zakaga wani waje da aka rubuta, Upload image da shuɗin rubutu.Kana dannawa, ze baka damar ganin duka zaɓar duka hotunan da suke cikin wayarka domin yi musu aiki. Da zaran ka danna zakaga ya ɗanyi loading kaɗan daga bisani kowani irin Background kai hoto a jiknsa zakaga ya fuddashi sannan ya baka damar ka sake zaɓo duka kalar Background ɗin da kake so.

YAYA ZAKA SAKA KOWANI BACKGROUND DA KAKE SO?


Kawai daga sama kan hotonka zakaga wani waje anrubta Edit kana dannawa ze baka kalolin Background kyauta wanda zaka saka, daga gefe kuma a hannunka na dama zakaga wajan kaloli, to anan ne zaka danna ka zaɓi duk wanda kake so.

Bayan ka gama zaɓa ya canza maka da kansa a gefe saman hannunka na dama zakaga wajan wata alama ta kibiya wato zaka sauke abunda ka gama yimasa aiki. Kana dannawa ze nuna maka ko kaimasa Share imaga ko kuma download seka dannawa wanda ya burgeka ko kuma kake so kayi.

Haƙika wanna App yanada kyau ace suna wayarka saboda wataran aikinsu ze taso maka da sauri, wanda ba lallai wani App ɗin ya maka wannan aikin ba a taƙaice da sauƙi sannan kuma a kyauta.

idan kanasan downloading wannan App ɗin


DANNA NAN
DANNA NAN
DANNA NAN


Bayan ka danna ze kaika Google play store kai tsaye zaka danna Install daga nan ze sauka a wayarka seka duba dukkan abunda muka nuna a saman bidiyonmu da kuma wannan darasin.

idan wannan darasin ya burgeka muna fatan zaka danna masa Like sannan kai share domi ƴan uwa su gani su amfana.

WA SALAM ALAIY,
MUN GODE.
CommentsFont Size
+
16
-
lines height
+
2
-